Hukumar kula da Shari'a ta dawo da Alƙali Umar Sunusi Ɗanbaba Dukurawa daga gudanar da aikin shari'a a Kano

Hukumar da ke kula da harkokin shari’a ta Jihar Kano, ta bayyana dawo da Alƙalin Babbar Kotun shari'ar muslunci ta Hoky, Dr. Alƙali Umar Sunusi Ɗan Baba Dukurawa, bakin aikin sa.
Wannan na cikin sanarwar Mai magana da yawun babbar Kotun Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya aiko wa Dala FM Kano, a ranar Litinin 6 ga Yuli, 2026.
Hukumar ta bayyana ɗaukar wannan mataki ne a taron ta na 90 da ta gudanar a ranar 3 ga watan Yuli, 2026.
Sanarwar ta ce taron ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin Babbar Jojin Kano Justice Dije Abdu Aboki, bisa la’akari da rahotanni da shawarwarin kwamitin karfar ƙorafe-ƙorafen jama’a na shari’a kan koke-koke da ladabtarwa da suka shafi alkalai da ma’aikatan kotunan jihar Kano.
Ɗaukar matakin dawo da Alƙali Dr. Umar Sunusi Ɗan Baba Dukurawa, na zuwa ne biyo bayan da hukumar ta kuma da ke kula da Shari'a ta jihar Kano, ta sake duba hukuncin da ta yanke tun da farko na cire shi daga gudanar da yin aikin shari’a a kwanakin baya.
Hukumar ta kuma ce bayan yin la’akari da ƙarin wasu takardu da kwamitin korafe-korafen jama’a na ɓangaren shari’a ya gabatar, waɗanda ba sa gaban hukumar a lokacin da aka yanke hukuncin da farko, hukumar ta lura cewa kwamitin bai ba da shawarar a sake kiransa ba.
A don haka, Hukumar ta yanke shawarar janye dakatarwar da aka yi wa Alƙali Dukurawa, daga yin aikin shari’a daga ranar 3 ga Yuli, 2026, tare da mayar masa da cikakken albashi da duk wani haƙƙi na ma’aikaci, tare da umartarsa da ya ci gaba da aikinsa na shari’a a kotunsa.
Sanarwar ta kuma ce, bayan tattaunawa na tsanaki, hukumar ta amince da daukar matakan ladabtarwa da suka dace da kundin tsarin mulkin kasar na tabbatar da gaskiya da rikon amana, da kuma amincewar jama'a kan gudanar da shari'a.
Hukumar ta kuma jaddada aniyar ta na ci gaba da bin ka’idojin ɗa’a, da ƙwarewa, da kuma ɗa’a a cikin harkokin shari’a na jihar Kano.
Ta kuma jaddada cewa dole ne jami'an shari'a da na kotuna su ci gaba da gudanar da ayyukansu ta hanyar da za ta sa jama'a su amince da gudanar da shari'a, tare da gargaɗin cewa duk wani aiki na rashin ɗa'a, da cin hanci da rashawa ko cin zarafi na ofishin zai jawo ɗaukar matakin da ya dace.



