Gwamnati ta shirya gano bindigogi sama da miliyan 6 da ke hannun ƴan Najeriya ba bisa ƙa'ida ba.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, tana ƙoƙarin gano bindigogi sama da miliyan shida da ake zargin suna hannun jama’a ba tare da izinin doka ba a ƙasar.
An ce matakin zai taimaka wajen gano makaman da ba a yi musu rajista ba, da kuma dakile laifukan da ake amfani da bindigogi wajen aikatawa.
Hukumomi sun bayyana cewa za a bukaci hadin kan jama’a wajen ganin an samu nasarar gano makaman da kuma karfafa tsaro a fadin kasar.



