Kotu ta bada umarnin kamo Hon. Aliyu Haidar kan zargin zamba da sayar da kadarorin bogi a Kano

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 24, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Mahmud, ta bayar da umarnin a kamo Hon. Aliyu Ibrahim Haidar, a duk inda yake domin gurfanar da shi a gaban kotun.
Tun da farko, Gwamnatin Jihar Kano ce ta shigar da ƙara a kan Haidar, bisa zargin damfara, da cuta da kuma sayar da kadarorin bogi da suka haɗa da filaye, kwangwaye, da gidaje da darajarsu ta kai kimanin naira miliyan 134.
An yi zargin cewa Haidar ya sayar da kadarorin ne ga wani mutum mai suna Alhaji Sani Abdullahi a unguwannin Ɗanbare, da ke yankin Kuyan Ta Inna, da kuma yankin Kan titin zuwa Sani Abacha Youth Centre a Kano.
Sai dai a zaman kotun na ranar Alhamis 4 ga Yuni, 2026, wanda ake ƙarar bai halarci kotun ba duk da cewa an sanar da shi ranar zaman shari’ar.
Lauyan Gwamnatin Jihar Kano, Barista Zahraddeen Hamisu Kofar Mata, ya roƙi kotun da ta bayar da umarnin kama Aliyu Ibrahim Haidar, yana mai cewa ya yi watsi da umarnin kotu duk da kasancewarsa cikin masaniyar ranar shari’ar, kuma jami’in kotu ya isar masa da takardar gayyata.
Bayan sauraron ƙorafin, kotun ta amince da buƙatar tare da bayar da umarnin kamo wanda ake ƙarar.
Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa ranar 16 ga watan Yuli, 2026.



