Mun dawo aikin yaƙi da ɓata gari gadan-gadan a Kano - Anti-Phone Snatching Force

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da kuma dakile ta’ammali da kayan maye, ta Anti - Phone Snaching Force da ke Kano, ta bayyana cewa jami’an ta sun dawo aiki gadan-gadan, sakamakon ƙoƙarin gwamnatin jihar kan yunƙurin magance ƙalubalen da suke fuskanta.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar a Kano, SK Ibrahim Garba Ahmad, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilinmu na ‘Yan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, a ranar Alhamis 18 ga watan Yuni, 2026.
A kwanakin baya ne dai jami'an rundunar suka bayyana dakatar da aikin yaƙi da ɓata gari a jihar nan, sakamakon ƙalubalen da suka ce suna fuskanta na rashin kula da walwalar su, da ƙarancin kayan aiki, da dai sauransu, inda suka ce sai gwamnatin Kano, ta magance musu ƙalubalen za su dawo bakin aiki.
SK Ibrahim Garba ya kuma ce yanzu haka jami’an rundunar sun shirya tsaf domin shiga lungu da sako na fadin jihar Kano, domin yaki da miyagun ayyuka kuma ciki har da fadan daba, da kwacen waya da sha da dillancin kayan maye.
Ibrahim Garba ya kara da cewa, yanzu haka gwamnatin jihar Kano ta dukufa wajen magance kalubalen da jami’an suke fuskanta na karancin kayan aiki, da batun biyan su albashi, da dai sauransu, bisa yadda kwamandan rundunar ta Kossap, Nura Salisu Sharada, ya tashi tsaye a kai.
A cewar sa, "Ƙoƙarin da Kwamanda Nura Salisu Sharaɗa ya yi, ya sa har Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya zauna da su tare da umarnin magance matsalolin da mu ke fuskanta, in ji Ibrahim.”
Ya kuma ce Kwamandan rundunar ta KOSSAP, Nura Salisu Sharaɗa, na buƙatar iyaye da su ƙara kula da shige da ficen ƴaƴansu, da ma sanin irin abokan su, domin gujewa lalacewar tarbiyyar su.
Wakilin namu Hassan Mamuda Ya’u ya ruwaito cewa, rundunar tsaron ta kuma gargadi dukkan matasan da suke addabar jama’a da miyagun ayyuka da su zubar da makaman su tare da rungumar zaman lafiya, domin gujewa abinda ka je ya dawo.



