Koma Labarai
Labarai

Fursunoni 61 sun sauke Al-kur'ani mai girma a gidan gyaran hali na Kurmawa a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Fursunoni 61 sun sauke Al-kur'ani mai girma a gidan gyaran hali na Kurmawa a Kano

Hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali ta ƙasa reshen jihar Kano, ta bayyana cewa fursunoni 61, sun yi saukar karatun Al-kur'ani mai girma a gidan gyaran hali na Kurmawa.

Jami'in hulɗa da jama'a na Hukumar a Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da ya aiko wa Dala FM Kano, a ranar Litinin 13 ga Yuli, 2026.

Ya kuma ce cikin mutanen da suka sauke littafin Al-kur'anin akwai maza 55, da kuma mata guda 6, waɗanda suka yi saukar a ranar Lahadi 12 ga Yuli, 2026.

Ya ce wannan na daga cikin ƙa'idar aikin hukumar na cewar duk mutumin da ya samu kan sa a gidan ajiya da gyaran hali a gyara masa halin sa domin ganin ya zama mutumin kirki.

A cewar sa, "Mutanen sun samu wannan dama ce ta haddace Al-kur'ani mai girma a gidan gyaran hali na Kurmawa, wanda hakan ya zama abin farin ciki sosai," in ji shi.

A jawabin sa mai kula da Hukumar Gidajen gyaran hali ta Jihar Kano, Ahmed Yusuf Lakpene, ya yabawa Babban Kwanturolan Hukumar Gidajen Gyaran hali ta ƙasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, bisa jagorancinsa da kuma ƙoƙarin da yake yi na bunƙasa shirye-shiryen ilimi, koyon sana'o'i da tarbiyya a gidajen gyaran hali na Najeriya.

A nasa ɓangaren, shugaban gidan gyaran hali na Kurmawa, DCC Ibrahim Isah Rambo Ibrahim, ya miƙa godiyar sa ga Gidauniyar Chokali Humanitarian, bisa gudunmawar da suka bayar har mutanen suka samu damar sauke Alkur'anin.

Domin ƙarfafa musu gwiwa, Hukumar Kula da Gidajen gyaran hali tare da haɗin gwiwar gidauniyar Chokali Humanitarian Foundation, sun rabawa waɗanda suka kammala karatun kayan tallafi da suka haɗa da sabbin kaya, katifu, barguna da kuma tallafin kuɗi domin sauƙaƙa musu komawa cikin al'umma bayan sun kammala zaman gidan gyaran hali.

Ready to PlayDala FM88.5 FM