Koma Labarai
Labarai

Majalisa ta yi karatu na biyu a ƙudirin dokar samar da hukumar majalisar masarautun Kano da Sarki Khalifa Muhammadu Sanusi II zai jagoranta

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisa ta yi karatu na biyu a ƙudirin dokar samar da hukumar majalisar masarautun Kano da Sarki Khalifa Muhammadu Sanusi II zai jagoranta

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi karatu na biyu a ƙudirin dokar samar da hukumar majalisar masarautun jihar.

Hukumar wacce ake sa ran za ta haɗe masarautun Kano baki ɗaya ƙarƙashin inuwa guda bisa jagorancin Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na II, inda zai yi aiki da sarakunan Gaya da Ƙaraye da kuma Rano.

Da yake karanta dokar, shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala, ya bayyana cewa ana zargin zare hannun masarautun gargajiya ya taka rawa wajen taɓarɓarewar harkar tsaro a jihar Kano.

Wakilinmu na majalisar dokokin Sunusi Shuaib Musa ruwaito cewa, majalisar ta kuma yi karatu na biyu na samar da wani sashe da zai kula da tsara birane da kuma cigaban ƙasa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM