Koma Labarai
Labarai

Majalisa ta amince da kafa hukumar samar da tashar wutar lantarki mai zaman kanta a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisa ta amince da kafa hukumar samar da tashar wutar lantarki mai zaman kanta a Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kafa hukumar samar da tashar wutar lantarki mai zaman kanta a jihar.

Majalisar ta amince da kafa hukumar ne bayan da kudirin ya tsallake karatu na uku a zaman ta na ranar Laraba 22 ga Yuli, 2026, tare da muhawara kan dokar, wacce za ta bai wa kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane damar zuba hannun jari.

Da yake ƙarin haske kan abinda dokar ta ƙunsa, shugaban masu rinjaye Lawan Husaini Dala, ya ce hukumar za ta bada damar ƙara haɓaka tattalin arzikin jihar.

Kazalika majalisar ta kuma karɓi ƙudurin gaggawa kan yawan sace kayan lantarki da ake yi musamman a yankunan karkara.

Ɗan majalisa mai wakiltar Madobi, Sulaiman Mukhtar Ishaq, ne ya gabatar da buƙatar hakan bayan da wasu ɓata gari suka shiga garin Madobi tare da sace muhimman kayan wuta.

Wakilinmu Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, Majalisar ta kuma umarci kwamitin wuta da ya bincika lamarin tare da gabatar da rahoton sa cikin wata guda.

Ready to PlayDala FM88.5 FM