Koma Labarai
Labarai

Hukumar Shari'a ta buƙaci a rinƙa gaggawar yanke hukunci a shari'u don sauƙaƙa wa maƙaraya a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hukumar Shari'a ta buƙaci a rinƙa gaggawar yanke hukunci a shari'u don sauƙaƙa wa maƙaraya a Kano

Hukumar Shari'a ta jihar Kano, ta ziyarci Alƙalin Alƙalai na jihar Kano, Dr. Tijjani Yusuf Yakasai, domin tattauna wa kan yadda za a magance matsalolin da ake fuskanta a harkokin Shari'a, tare da daƙile jinkiri a shari'a a kotuna, tare da saurin yanke hukunci a kan shari'ar bashi da gado da sauransu.

Ziyarar shugabannin hukumar shari’ar ta gudana ne a larabar nan, inda bangarorin biyu suka tattauna mahimman batutuwa a ofishin Alkalin Alkalan na jihar Kano, Dr. Tijjani Yakasai.

Tattaunawar tasu ta mayar da hankali ne a kan yadda za a lalubo hanyoyin magance matsalolin da ake fuskanta a harkokin shari’a, da kuma saurin warware shari’ar bashi da ta auratayya da sauransu, domin kara samar da sauki a tsakanin maƙaraya.

Da yake karin bayani a yayin ziyarar, shugaban hukumar shari’a ta jihar Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ya ce akwai bukatar a rinka gaggawar yanke hukunci a kan shari’un da suke bukatar gaggawa musamman ma irin na fadan daba, da kwacen waya da kuma ta’ammali da kayan maye, duba da yadda matsalar ke ci gaba da addabar jama’a a jihar Kano.

Shima a nasa banagren, Alkalin Alakalai na jihar Kano, Dr. Tijjani Yusuf Yakasai, ya ce matukar ana son a kawo karshen yawaitar aikata manyan laifuka a sasan jihar nan musamman ma na kisan kai, sai Gwamnati ta tashi tsaye wajen zartas da hukunci a kan mutanen da kotu ta yankewa hukuncin kisa.

Dr. Tijjani Yusif Yakasai ya kuma ce tara masu ruwa da tsaki wajen zama na musamman domin fito da matsalolin da ake fuskanta a harkar shari’a da jami’an tsaro, ka iya taimakawa wajen magance kashe rayuka a sassan jihar.

A nasa jawabin, Kwamishina na biyu a hukumar shari’a ta jihar Kano, Sheikh Ali Danabba, ya ce hukumar za ta kara himma wajen ganin an dakile sha da dillancin miyagun kwayoyi a fadin jihar nan, domin tabbatar da gyaruwar tarbiyyar matasa.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa a yayin ziyarar dai shugaban hukumar shari’ar ta jihar Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, na tare da Kwamishina na biyu a hukumar Gwani Dahiru Yakasai, da Daraktocin hukumar da ma’aikata dai sauransu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM