Koma Labarai
Tsaro

Rundunar tsaro ta Anti-Phone Snatching Force Kano, ta kama matashi Suda, kan zargin haddasa faɗan daba a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rundunar tsaro ta Anti-Phone Snatching Force Kano, ta kama matashi Suda, kan zargin haddasa faɗan daba a Kano.

Rundunar tsaro ta Anti-Phone Snatching Force a Kano, ta samu nasarar cafke wani matashi a unguwar Kuntau Ɗorayi Babba, wanda ake zargi da haddasa fadace-fadacen daba a wasu sassan jihar nan.

Hakan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ga manema labarai a Kano.

Sanarwar ta ce a bisa bayanan sirrin da suka samu, ana zargin matashin, wanda aka fi sani da Suda, da hannu wajen tayar da tarzoma da haddasa rashin zaman lafiya a yankuna da dama na jihar Kano.

Kazalika Sanarwar ta kuma ce, rundunar ta tabbatar da cewa an kama wanda ake zargin ne a wani samame da jami'anta suka gudanar a ranar Litinin 20 ga Yuli, 2026, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken matsayinsa da kuma waɗanda ke da hannu a lamarin.

A cewar sanarwar, Kwamandan rundunar ta Anti-Phone Snatching Force Kano, Nura Salisu Sharaɗa, ya jaddada ƙudirin rundunar na tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Nura Sharaɗa ya kuma yi kira ga jama'a da su ci gaba da bai wa jami'an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai a kan duk wani abu da zai iya kawo barazana ga tsaro.

Ready to PlayDala FM88.5 FM