Fitaccen Ɗan kasuwa da ke Kano, Alhaji Audu Manaja, ya rasu.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Fitaccen ɗan kasuwa a Kano, da ya yi fice a fannin man fetur, Alhaji Abdullahi Ahmad, da aka fi sani da Audu Manaja, ya rasu a birnin Cairo bayan doguwar jinya.
Iyalan marigayin sun shedawa manema labarai cewar, ana sa ran yin jana'izarsa ranar Juma'a, a masallacin Jami'ur Rahma da ke Kundila, bayan idar da Sallar Juma'a idan Allah ya sa an iso da gawar sa akan lokaci.
Marigayi Alhaji Audu Manaja, ya yi ƙaurin suna ta fuskar hada-hadar dillancin man fetur da harkokin filaye da gidaje.
Gidajen man sa da ke amsa sunasa suna da dama a Kano, da wasu sassa na arewacin Najeriya.
Marigayi Audu Manaja, yana cikin 'yan kasuwar Kano da Allah ya yi musu nasibi a duk harkar kasuwancin da suka shiga a faɗin ƙasar, da ma wasu yankunan duniya.



