Koma Labarai
Shari'a

Kotun Abuja ta ɗage sauraron ƙarar sakin auren Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotun Abuja ta ɗage sauraron ƙarar sakin auren Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.

Wata kotun Upper Area Court da ke Gudu a Abuja, ta ɗage sauraron ƙarar neman sakin auren Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da matarsa Zainab, zuwa ranar 15 ga watan Disamban 2026.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnan bai halarci zaman kotun na ranar Talata 17 ga watan Nuwamba, 2026, ba.

Zainab, wadda ’yar tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ce, ita ce mata ta biyu ga Abba Kabir Yusuf.

Ta shigar da ƙarar neman sakin auren ne a kotun da ke Abuja.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM