Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta ɗaure ɓarawon babura watanni 77 a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta ɗaure ɓarawon babura watanni 77 a Kano.

Kotun majistret mai lamba 21 ƙarƙashin jagorancin mai Shari'a Muttaƙa Ɗandago, ta hori wani matashi mai suna Mubarak Lawanda, da ɗaurin watanni 10 a laifin sata da kuma watanni 6 a laifin haurawa gida, sai kuma watanni 14 ko biyan kuɗin babur ɗin da ya sata.

Hukuncin na zuwa ne yayin zaman kotun na ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba, 2026.

Haka kuma, kotun ta sake ɗaure matashin watanni 6 a laifin sata, da watanni 15 a laifin shiga gida ba da izini ba, da kuma watanni 15 ko biyan kudin baburin da ya sata.

Kazalika, kotun ta ƙara yi wa matashin ɗaurin watanni 5 a laifin sata, da ɗaurin watanni 6 a laifin kutse.

Tun da farko yansanda ne suka gurfanar da matashin mai suna Mubarak Lawan, inda ake tuhumar sa da laifin haurawa gidajen mutane yana sace musu babura a unguwar Bachirawa.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewa kotun ta ayyana cewar ɗaurin zai tafi tare ne gaba ɗaya.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM