Koma Labarai
Tsaro

Za mu ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Kano - Ƴan Sanda

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Za mu ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Kano - Ƴan Sanda

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta yaba wa al'umma, da gwamnatin jihar Kano, da ɓangaren masarauta, bisa gudunmawar da aka bayar har ake ci gaba da gudanar da bikin Babbar Sallah lafiya.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa Dala FM Kano, a ranar Juma'a 29 ga Mayu, 2026.

Ya ce ana gudanar da bukukuwan Babbar Sallar ne sakamakon gudunmawa, da kuma haɗin kan da dukkan ɓangarorin suka bayar, tare da bin shawarwarin da ake baiwa al'umma.

Sanarwar ta kuma ce, Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, na ƙara tabbatar wa al'umma cewa, rundunar a tsaye take domin ci gaba da tabbatar da tsaro, da zaman lafiya a faɗin jihar Kano, baki ɗaya.

"Mu na kira ga al'umma kan cewar duk inda aka ga wani motsi, ko abinda ba a yarda da shi ba, ko kuma zargin abinda ka iya kawo rashin tsaro, a yi hanzarin sanar da jami'an mu a ofishi mafi kusa, ko a kira ƴan sanda ta 08032419754, ko 08123821575, ko kuma 09029292926, in ji Kiyawa.”

Rundunar ƴan sandan ta kuma yaba wa sauran jami'an tsaro da ke jihar Kano, bisa aikin da suke yi na bada gudunmawa, da jajircewa wajen aikin kare rayuka, da dukiyoyin al'umma.

Ready to PlayDala FM88.5 FM