Koma Labarai
Tsaro

Ƴan Sanda sun sake kama Auwalu Ɗan daba, ɗauke da Makami da tabar wiwi bayan fitowar sa daga gidan yari a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƴan Sanda sun sake kama Auwalu Ɗan daba, ɗauke da Makami da tabar wiwi bayan fitowar sa daga gidan yari a Kano

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta sake cafke matashi Auwalu, da ake yi wa laƙabi da Auwalu Ɗan daba, mazaunin Ɗorayi unguwar Bello, ɗauke da makami da kuma Tabar Wiwi.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Kakakin rundunar a Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Asabar 11 ga Yuli, 2026.

Ya ce an sake kama Auwalu Ɗan daba, ne bayan fitowar sa daga gidan ajiya da gyaran hali a jihar Kano, inda aka kama shi ɗauke da Tabar Wiwi da kuma Makami.

Ready to PlayDala FM88.5 FM