Koma Labarai
Tsaro

Gamayyar Matasan Kano ta buƙaci a gaggauta bincike tare da ɗaukar mataki kan kisan gillar da aka yi wa Ɗanshagamu.

Hassan Mamuda Ya'u 24 views
Gamayyar Matasan Kano ta buƙaci a gaggauta bincike tare da ɗaukar mataki kan kisan gillar da aka yi wa Ɗanshagamu.

Ƙungiyar Gamayyar Matasan Kano, ta buƙaci a gaggauta gudanar da binciken tare da ɗaukar matakin da ya dace a kan duk wanda aka samu da hannu a kashe Ɗan jaridar nan Ibrahim Khalil Ɗanshagamu.

Shugaban Ƙungiyar, Alhaji Muhammad Tijjani Ɗorayi (MTD) ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Dala FM Kano, ranar Alhamis 10 ga watan Satumba, 2026.

Ya ce akwai abin takaici kan yadda aka samu wasu ɓata gari suka haura gidan Marigayi Ibrahim Khalil, da ke unguwar Gaida, suka yi masa kisan gilla ta hanyar yankan rago a cikin daren Talata 8 ga Satumba, 2026.

Yanzu haka dai rundunar ƴan sandan Kano, ta bakin Kakakin ta CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta bayyana cewa ta kama mutane biyu waɗanda ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa Ɗanshagamu.

Muhammad Tijjani Ɗorayi ya kuma yi kira ga gwamnatin Kano, da Kwamishinan ƴan sandan jihar Ibrahim Adamu Bakori, da sauran masu ruwa da tsaki kan su tabbatar an gudanar da cikakken bincike tare da ɗaukar mataki a kan duk wanda aka samu da hannu a kisan.

A cewar sa, "Ɗanshagamu mutumin kirki ne wanda yake da ƙokari wajen samar da ci gaban al'umma, bai kamata jinin sa ya tafi a banza ba, ya kamata a yi abinda ya dace a kan kisan gillar da aka yi masa," in ji shi.

Daga bisani, Muhammad Ɗorayi ya ce a madadin Ƙungiyar Gamayyar Matasan Kano, suna miƙa saƙon ta'aziyyar su ga iyalan marigayi Ibrahim Khalil Ɗanshagamu, da Hakimin Gundumar Ɗorayi, Alhaji Shehu Kabir, ya yi addu'ar Allah ya gafarta musu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM