Al'ummar unguwar Gaida layin Abacha, sun gudanar da gangami don a yi musu adalci kan waɗanda ake zargi da satar babura a yankin

Al'ummar unguwar Gaida layin Abacha da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, sun gudanar da wani gangami domin nuna damuwar su dangane da yawan sace-sacen baburan da ake yawan yi musu a unguwar.
Mazauna yankin sun gudanar da gangamin ne a safiyar Lahadin nan, inda suka miƙa koken su ga mai unguwar su Mallam Fatihu Basaja, don ya miƙa zuwa wajen na gaba da shi wajen ganin an ɗauki matakin da ya dace akan wanda ake zargi da kitsa satar babura a yankin mai suna Mansur S Gaye.
Al'ummar unguwar dai sun bayyana damuwar tasu ne biyo bayan da rundunar tsaro ta Civil Defense ta ƙasa NSCDC, reshen jihar Kano, ta sanar da kama wani mutum mai suna Mustapha Sani a gidansa da ke Gaida layin Abacha, bisa zargin sa da satar babur samfurin roba-roba.
Sai dai da aka bi diddigin aka samu wasu kayayyaki a gidan sa, da suka haɗar da lambobin babura guda 11, da Sukundireba guda 6, sai wasu damun mukullayen babura guda 3.
Kan zargin da al'ummar unguwar ta Gaida Layin Abacha, ke yi wa Mansur S Gaye, ne ya sa suka yi gangamin domin miƙa koken su domin ganin an tabbatar da adalci a kan mutumin da aka kama kan satar Bauran, tare buƙatar a kama S Gaye, domin gudanar da bincike a kan sa, a kuma tashe shi daga unguwar da suke.
Da yake miƙa takardar koken a madadin al'ummar yankin ga Mai unguwar Gaida layin Abacha, wato Mallam Muhammad Sani, ya ce sun miƙa koken nasu ne domin ganin an daƙile sace-sacen Bauran da ake yi musu a unguwar su.
A nasa ɓangaren, Mai unguwar Gaida layin Abacha da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, Mallam Fatihu Shehu wanda akafi sani da Basaja, ya ce ya karɓi takardar ƙorafin al'ummar yankin kuma zai miƙa ta ga Dagacin yankin domin ya miƙa ta ga Hakimi, shi kuma ya miƙa ta zuwa ga Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II.
A cewar sa, za su yi duk mai yiyuwa domin ganin mahukunta sun sharewa al'ummar sa hawaye, bisa yadda suka nuna damuwa a kan wanda ake zargi da hannu wajen kitsa satar babura a yankin, domin tabbatar da adalci a tsakani.
Kan hakan ne muka yi duk mai yiyuwa domin ji daga ɓangaren Mansur S Gaye, sai dai haƙan mu bai cimma ruwa ba, amma da zarar ya magantu za a ji mu da shi.



