Koma Labarai
Tsaro

Al'ummar unguwar Tudun Yola sun samar da ofishin Civil Defense domin yaƙi da ɓata gari a yankin su.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Al'ummar unguwar Tudun Yola  sun samar da ofishin Civil Defense domin yaƙi da ɓata gari a yankin su.

Al’ummar unguwar Tudun Yola ƙarshen kwalta da ke Kano, sun yi namijin ƙoƙari wajen samar wa kansu tsaro, domin daƙile ayyukan bata-gari da ke neman lalata zaman lafiya a yankin.

An buɗe wani ofishin tsaro ƙarƙashin jagorancin jami’an Civil Defence domin ƙarfafa tsaro da haɗa kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da ofishin, wakilin Kwamandan Civil Defence na Jihar Kano, kuma Area Commander na Metro, Kabiru Garba Fagge, ya ce haɗin kan jama’a da jami’an tsaro ne kaɗai zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro.

Shi ma shugaban ƙungiyar ci gaban yankin, Ahmad Hashim, ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ne bayan shawarar da suka samu daga DPO na Rijiyar Zaki, wanda ya ba su shawarar samar da ƙofofin tsaron unguwa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.

Ready to PlayDala FM88.5 FM