Koma Labarai
Labarai

Shugabanni ku mutunta kare haƙƙin bil'adama da tabbatar da adalci ga al'umma - Human Rights

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Shugabanni ku mutunta kare haƙƙin bil'adama da tabbatar da adalci ga al'umma - Human Rights

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Center for Human Rights and Charity Development initiatives, ta buƙaci shugabanni da ma sauran al'umma da su yi koyi da darussan Hijira na hakuri, tare da mutunta kare haƙƙin bil'adama, da tabbatar da adalci a cikin al'umma.

Babban Daraktan Ƙungiyar a ƙasar nan Kwamared Dr. Auwal Jibril Maifada, ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da ya aikowa Dala FM, Talatar nan, a wani ɓangare na taya al'ummar musulmi murnar shiga sabuwar shekarar musulunci ta 1 ga watan Muharram, 1448.

Ya kuma yi addu'ar Allah ya sanya wannan sabuwar shekara ta musulunci ta 1448, ta zama mai albarka, da zaman lafiya, da kuma ci gaba da haɗin kai da taimakon juna.

Ya kuma yi kira ga shugabanni da su ƙara tashi tsaye wajen bin dukkan matakan da suka dace domin ganin an daƙile matsalolin tsaron da ke addabar yankin arewacin Najeriya.

Ya kuma yi wa dukkanin al'ummar Musulmi Barka da shiga sabuwar shekarar musulunci ta 1448, inda ya yi fatan jama'a za su ƙara mayar da hankali wajen yin abinda ya kamace su domin goben su ta yi kyau.

Ready to PlayDala FM88.5 FM