Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin yaƙi da satar fitilun tituna da lalata su a jihar

Gwamnatin Kano ta kafa wani kwamiti na musamman domin yaƙi da satar fitilun tituna da kuma lalata su a sassan daban-daban na faɗin jihar.
Kwamishinan Ayyuka na jihar, Marwan Ahmed, ne ya bayyana hakan yayin wata hira kai tsaye da gidan rediyon jihar Kano, kamar yadda Mai Ɗauko wa Gwamna Rahoto a ma’aikatar, Khamis Bashir Bako Ayagi, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce Kwamishinan ya bayyana cewa, kwamitin zai rinƙa gudanar da sintiri dare da rana domin sa ido kan fitilun tare da gano masu satar su ko lalata su.
Ya kuma gargaɗi cewa duk wanda aka kama yana satar fitilun zai fuskanci hukunci, yayin da za a tilasta wa duk wanda ya lalata fitila da motarsa ya biya kuɗin gyara ko sauya ta.
Haka kuma, ya buƙaci al’umma su taimaka wajen kare kayayyakin gwamnati tare da kai rahoton duk wani motsi da ake zargin yana da alaƙa da satar fitilun ko lalata su ga hukumomin da abin ya shafa.



