Koma Labarai
Tsaro

DSS ta kama matashi ɗauke da bindigogi AK-47 guda 3, da Bama-bamai, da kuma kwason harsasai a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
DSS ta kama matashi ɗauke da bindigogi AK-47 guda 3, da Bama-bamai, da kuma kwason harsasai a Kano

Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta ƙasa (DSS) reshen jihar Kano, ta kama wani matashi mai suna Abubakar Muhammad, bisa zargin sa da safarar makamai masu haɗari, zuwa garin Funtua da ke Jihar Katsina.

Jami’an na DSS sun kama wanda ake zargin ne a Ƙaramar Hukumar Gezawa bayan samun bayanan sirri da suka kai ga tare shi yayin da yake ƙoƙarin jigilar makaman zuwa inda aka tura shi.

Makaman da aka ƙwato daga hannunsa sun haɗa da bindigogin AK-47 guda uku, da Bama-bamai na makamin roka (RPG) guda huɗu, da kuma kwanson harsasai guda biyu.

Majiyoyi sun ce binciken farko ya nuna cewa an ɗora wa Abubakar aikin jigilar makaman ne daga yankin Maigatari da ke Jihar Jigawa zuwa Funtua, inda aka yi masa alkawarin biyan Naira 450,000 bayan ya kai kayan ga wanda ake sa ran zai karɓe su.

Da yake amsa tambayoyin jami’an tsaro, wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne ke jigilar makaman, inda ya ce da farko ya ƙi karɓar aikin, amma daga bisani ya amince bayan matsin lambar da aka ci gaba da yi masa.

Ya kuma yi ikirarin cewa bai taɓa shiga irin wannan aiki a baya ba, tare da nuna nadama kan lamarin, kamar yadda kafar Indaranka ta ruwaito.

A cewar DSS, kamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka nuna motsin wanda ake zargin a hanyar Kano zuwa yankin Funtua, wani yanki da ke fama da matsalolin tsaro da hare-haren ‘yan bindiga.

Hukumar ta ce za ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, yayin da ake ci gaba da neman sauran mutanen da ake zargin suna da alaƙa da safarar makaman.

DSS ta kuma tabbatar da cewa tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin gano tare da rusa hanyoyin safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, domin inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Arewa maso Yamma da ƙasa baki ɗaya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM