Gwamnatin Kano ta shirya karɓar ƙorafe-ƙorafen masu filaye, gidaje da gonaki a Rimin Zakara.

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta shirya karɓar ƙorafe-ƙorafen masu filaye da gidaje har ma da gonaki a garin Rimin Zakara da ke kusa da jami'ar Bayero a jihar, Kasancewar yanzu haka ma'aiatar na cigaba da tantance mutanen don cigaba da biyan su diyya.
Kwamishinan ma'aikatar ta ƙasa da tsara birane na jihar, Abduljabbar Muhammad Umar Garko ne, ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai, jim kaɗan da duba yadda aikin tantancewar ke gudana a ma'aikatar a ranar Asabar.
Abduljabbar Garko, ya kuma ce yanzu haka, ma'aikatar kasa ta tantance fiye da Mutane 200 wanɗanda za su je hukumar tsaron farin kaya DSS, domin tabbatar da sahihancin bayanan da suka bayar kafin karbar diyyar.
Ya ce an yi hakan ne domin kaucewa irin abun da ya faru a baya kafin wannan lokaci don ganin an danka hakki ga mai shi.
A cewar sa, a baya da aka tantance mutane 200, amma a hukumar DSS, iya mutane 70, ne suka iya zuwa saboda yadda wasu da basu da alaƙa da guraren suka kasance a cikin mutane 200, a baya.



