Koma Labarai
Tsaro

Yan sanda sun kama Usman Ibrahim da ake zargi da damfarar miliyan 171, bayan ayyana nemansa ruwa a jallo.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Yan sanda sun kama Usman Ibrahim da ake zargi da damfarar miliyan 171, bayan ayyana nemansa ruwa a jallo.

Rundunar ƴan sandan Najeriya, shiyya ta ɗaya (Zone One) da ke Kano, ta bayyana kama Usman Ibrahim, mutumin da ta bayyana tana nema ruwa a jallo.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar Abdullahi Hussain, ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a 25 ga watan Satumban 2026.

Ƴan sandan dai suna zargin Usman Ibrahim ne da damfarar Naira miliyan 171, lamarin da suka bayyana neman sa ruwa a jallo, inda daga bisani suka cafke shi.

Idan dai ba a manta ba, wani lauya mai suna Barrister Shua'ibu Gama ya ce bayyana Usman Ibrahim a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo da yansandan shiyya ta daya (Zone One) suka yi ya saɓa da tsarin doka.

Lauyan ya bayyana cewar akwai umarni da babbar kotun jaha ta bayar tun a ranar 12 ga watan Agustan 2026, a kan cewar kada yansandan su kama shi, duk wani mai ƙorafi akan Usman to ya je a hadu a kotu.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM