Koma Labarai
Shari'a

Zargin kashe Ɗansanda: Kotu ta aike da matasa 11 gidan gyaran hali a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Zargin kashe Ɗansanda: Kotu ta aike da matasa 11 gidan gyaran hali a Kano.

Kotun majistret mai lamba 2 ƙarƙashin jagorancin mai Shari'a Auwal Yusuf Sulaiman, ta aike da wasu matasa 11 gidan gyaran hali da tarbiyya.

Ana dai zargin matasan ne da laifin haɗa baki da tayar da hankalin al'umma da kuma ƙeta ta hanyar kunna wuta a kan kayan mutane, da kuma kashe jam'i'in yansanda.

Ƙunshin zargin ya bayyana cewar an samu rashin fahimtar juna akan batun iyakar gona a ƙaramar hukumar Wudil da ke Kano, lokacin da yansanda suka je wajen domin tabbatar da doka da oda, inda aka yi zargin cewar wasu matasa goma sha ɗaya sun haɗa baki sun kashe wani ɗansanda.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewaz an kuma zargi matasan da laifin cinna wuta akan kayan al'umma.

Kotun ta bayyana cewar bata da hurumin yin shari'ar kisan kai sai an jira shawarar lauyoyin gwamnati, an kuma sanya ranar 15 ga watan gobe domin ƙara gabatar da matasan.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM