Koma Labarai
Tsaro

A shirye muke wajen tunkarar masu faɗan daba a unguwannin Kano - Bijilante

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
A shirye muke wajen tunkarar masu faɗan daba a unguwannin Kano - Bijilante

Rundunar yan sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ta bayyana shirin ta na tunkarar ɓata garin matasa masu Fadan Daba a unguwannin Kano, domin ƙara wanzar da zaman lafiya a jihar.

Babban Kwamandan rundunar a Kano, Alhaji Shehu Muhammad Rabi'u, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai a ranar Laraba 3 ga Yuni, 2026.

Sai dai ya ce rashin kayan aikin da za su yi amfani da su wajen yaƙi da masu faɗan daba, Shaye-shayen miyagun kwayoyi, da kuma ƙwacen wayoyin jama'a, na daga cikin babban ƙalubalen da suke fuskanta wajen tunkarar ɓata garin.

Shehu Rabi'u ya kuma buƙaci Gwamnatin Kano da masu hannu da shuni, tare da ƴan kasuwa da su taimaka wa jami'an rundunar da kayan aiki, domin samun dama wajen cigaba da kare rayuka da dukiyoyin Al'ummar kano baki ɗaya.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, a ƙarshe Shehu ya kuma yi kira ga daukacin Al'umma da su dinga bayar da bayanan sirri da zarar sunga motsin abinda basu yarda da shi ba, domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM