Koma Labarai
Labarai

Mazauna Ɗorayi sun miƙa ƙorafinsu ga Hukumar tace Fina-finai ta Kano, kan kafa Film House, a yankin su

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mazauna Ɗorayi sun miƙa ƙorafinsu ga Hukumar tace Fina-finai ta Kano, kan kafa Film House, a yankin su

Al’ummar unguwar Ɗorayi Ƙarama da maƙwaftanta sun miƙa ƙorafin su ga Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano, inda suka bayyana rashin amincewarsu da shirin samar da Film House a yankin.

Hakan na zuwa ne bayan wani zama na musamman da ƙungiyoyin ci gaban yankin suka gudanar, waɗanda suka haɗa da Centre for Community Support and Human Development, da Gidauniyar Mata Musulmi ta Kano, Community Build and Raise Initiative Hub.

Sauran sun haɗar da Ƙungiyar Arewa Mu Tashi Mu Farka, da kuma Danfodiyo Islamic Center, tare da haɗin gwiwar dattawa, da masu gidaje, da kuma limamai da sauran masu ruwa da tsaki a yankin.

Da yake jawabi a madadin al’ummar yankin, ɗaya daga cikin dattawan Ɗorayi, Dakta Yusif Ibrahim, ya bayyana damuwa kan yiwuwar tasirin aikin ga tsaro, da zaman lafiyar mazauna yankin da kuma tarbiyyar matasa, musamman idan aka yi la’akari da ƙalubalen tsaro da yankin ya fuskanta a baya.

Kungiyoyin da mazauna yankin sun ce sun kuma miƙa kwafin ƙorafin nasu ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwale, da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, da kuma Hukumar DSS, da Hukumar Hisbah ta jihar Kano.

Sauran sun haɗar da Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Kano, Ma’aikatar Shari’a, Majalisar Malamai da kuma Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, tare da sauran hukumomin da abin ya shafa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM