Koma Labarai
Labarai

Babbar Jojin Kano ta yi umarnin a saki fursunoni 7 daga gidajen gyaran hali a jihar sakamakon matsalolin lafiya.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Babbar Jojin Kano ta yi umarnin a saki fursunoni 7 daga gidajen gyaran hali a jihar sakamakon matsalolin lafiya.

Alkaliyar babbar kotun Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta bayar da umarnin sakin fursunoni bakwai bisa dalilan rashin lafiya, bayan da ta duba shari’o’in mutane 82 da ke tsare suna jiran shari’a.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa, reshen jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Ƙofar Nassarawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a 14 ga watan Agusta, 2026.

Sanarwar ta ce an gudanar da aikin duba shari’o’in a gidajen gyaran hali na Kurmawa da Goron Dutse, a wani mataki na hanzarta gudanar da shari’a da kuma kare haƙƙin mutanen da ke tsare.

Sanarwar ta kuma ce Mai Shari’a Abdu Aboki, ta duba shari’o’in mutanen da wasu daga cikinsu suka shafe shekaru a tsare ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu bisa ƙa’ida ba.

A yayin aikin, babbar mai shari'ar ta bayar da umarnin sakin fursunoni guda bakwai nan take saboda matsalolin lafiya, bayan la’akari da yanayin lafiyarsu da sauran abubuwan da suka shafi ci gaba da tsare su.

Mai Shari’a Abdu Aboki ta kuma jaddada muhimmancin gudanar da shari’a cikin adalci ba tare da jinkiri ba.

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa reshen Jihar Kano, Ahmed Lakpene, ya shawarci waɗanda aka saki da su ɗauki ’yancinsu a matsayin wata dama ta fara sabuwar rayuwa, su kasance masu bin doka tare da guje wa duk wani abu da zai iya sake kai su ga cin karo da doka.

Lakpene ya kuma yaba wa Babban Kwamandan Hukumar Gyaran Hali ta ƙasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, bisa samar da yanayin da ke ba da damar kula da fursunoni cikin mutunci, kamar yadda kafar Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya kuma ce ayyukan sakin fursunoni na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage cunkoso a gidajen gyaran hali da kuma tabbatar da cewa kowa yana samun damar yin adalci.

Ready to PlayDala FM88.5 FM