Satar gawayi: kotu ta ɗaure matashi tare da tsalala masa bulala goma a Kano
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Kotun shari'ar Muslunci mai zaman ta a Ɗanbare, Kano, ƙarƙashin jagorancin mai Shari'a Ibrahim Musa Abubakar, ta hori matashi Sani Muhammad, da ɗaurin watanni biyu ko zaɓin tarar naira dubu 20 da kuma bulala goma.
Ana tuhumar matashin ne da laifin satar gawayi buhu goma, sai dai matashin ya yi iƙirarin cewa buhu biyu da rabi ya sata.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewar, matashin mai suna Sani Muhammad ya yi rantsuwa da Alkur'ani a kan cewar ba buhu goma ya sata ba.



