Sarkin Kano ya hori dagatai 3 da ya naɗa da su zauna lafiya da al'ummar su.

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya naɗa sabbin dagatai guda uku da suke daga yankin gundumar Kunya a karamar hukumar Minjibir, inda aka naɗa Shamsu Aminu a matsayin dagacin Garke, da Abdulhamid Muhammad a matsayin dagacin garin Tsage.
Sarkin ya kuma naɗa Malam Nadabo Lawan a matsayin dagacin garin dogon kawo da ke ƙaramar hukumar Doguwa.
Bayan kammala naɗin nasu ne mai maraba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya hore su da su zauna lafiya da al'ummarsu, tare da sanya idanu a kan harkokin tsaro da lafiya da ilimi a garuruwansu.
Da yake jawabi dagacin garin Dogon Kawo a ƙaramar hukumar doguwa Malam Nadabo Lawan, ya bayyana farin cikinsa bisa naɗashi da mai maraba sarkim na Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi a matsayin dagacin.
Ya kuma ce zai gudanar da aikinsa bisa gaskiya da rikon amana tare da kira ga al'ummar garin nasa da su ba shi haɗin kai da goyon baya a kowane lokaci.
Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da'u Abdullahi ya rawaito cewa, al'umma daban-daban daga ƙananan hukumomin Kano sun halarci taron naɗin dagatan da ya gudana ranar Alhamis, a fadar masarautar Kano.



