Ƙungiyar Gamayyar Matasan Kano, ta karrama Sarkin Gaya, Dr. Aliyu Ibrahim, bisa ƙoƙarin sa a magance matsalar tsaro da samar da ci gaban al'umma.

Ƙungiyar Gamayyar Matasan Kano, haɗin gwiwa da Kwamitin tsaro na unguwanni Ɗorayi da kewaye, sun karrama Mai Martaba Sarkin Gaya, Dr. Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya, da shaidar girmama wa a gidan sa da ke yankin Ɗorayi.
Da yake jawabi ga manema labarai, Shugaban Ƙungiyar Gamayyar Matasan Kano, Alhaji Muhammad Tijjani Ɗorayi (MTD) ya ce sun karrama Mai martaba Sarkin Gaya, Dr. Alhaji Aliyu Ibrahim, ne bisa irin gudunmawar da yake basu kan sha'anin tsaro da kuma samar da ci gaban al'ummar unguwannin, da na yankin sa, da ma jihar Kano baki ɗaya.
Ya kuma yabawa Sarkin, da Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II, da sauran sarakunan Kano, da masu riƙe da dagacin Ja'en, da ma masu unguwannin yankin bisa irin ƙoƙarin da suke yi wajen ganin an magance matsalolin tsaro a yankin Ɗorayi, da kewaye, da ma jihar Kano.
A nasa jawabin, Mai martaba Sarkin Gaya, Alhaji Dr. Aliyu Ibrahim Gaya, ya bayyana jin daɗin sa da ziyara, gami da karrama shi da Kungiyar Gamayyar Matasan Kano, ta yi,
Sarkin ya kuma buƙaci Gamayyar matasan da su ci gaba da haɗa kai wajen samar da cigaban yankin Ɗorayi, da ma jihar Kano baki ɗaya, tare da baiwa hukumomin gudunmawa don ƙara magance matsalar tsaro a faɗin jihar.
Shima a nasa ɓangaren, Shugaban gamayyar kwamitin tsaro na unguwannin Ɗorayi da kewaye, Mallam Abdullahi Idris Ɗan Fodiyo, ya ce ƙoƙarin da Sarkin yake yi a harkar tsaro, da kuma ci gaban matasa da sauran ɓangarorin al'umma ya sa suka ga dacewar su karrama shi.
Yayin zirar da ta gudana a ranar Lahadi 23 ga Agustan 2026, ɓangarorin sun sha alwashin ƙara samar da ci gaban al'ummar jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.



