Koma Labarai
Labarai

Ba mu amince ayi naɗi a lokacin zaɓen NUT, na Kano ba - Ƙungiyar VCTF

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ba mu amince ayi naɗi a lokacin zaɓen NUT, na Kano ba - Ƙungiyar VCTF

Ƙungiyar Muryar Malaman Makarantun Firamare ta jihar Kano, wato Voice Concern teachers forum, ta ce ba ta amince a yi naɗi a lokacin zaɓen ƙungiyar Malamai ta ƙasa NUT reshen jihar Kano ba,

Shugaban ƙungiyar ta (VCTF) a Kano, Kwamared Abbas Adamu, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Kano.

Ya ce sun lura da cewa jagororin ƙungiyar ta NUT, sun yi shiru ba sa maganar shirye-shiryen gudanar a zaɓen ƙungiyar, duk kuwa da yadda yake bai fi saura wata ɗaya ba a gudanar da zaɓen.

A cewar sa, "A lokacin wancan zaɓen shekaru huɗu da suka gabata, masalaha aka yi, inda aka yi naɗi mai-makon zaɓe, abinda mu ke ganin na tauye haƙƙin mambonin ƙungiyar musamman ma ga masu sha'awar tsayawa takara," in ji shi.

Kwamared Abbas Adamu ya buƙaci mahukunta da su tsaya kai da fata domin ganin an gudanar da zaɓe idan lokacin ya yi, saɓanin ɗauki ɗora, domin tabbatar da adalci a tsakanin ƴan ƙungiyar ta NUT.

Ya kuma ce a dokar ƙungiyar kowanne mamba yana da damar tsayawa takara matuƙar ya cancanta, kuma kyauta ake bayar da fom ɗin tsayawa takarar, domin a dama da shi, kuma fom ɗin kyauta ne.

Abbas ya kuma yi kira ga shugabancin ƙungiyar ta NUT, reshen jihar Kano, da ya tabbata an gudanar da zaɓe idan watan Agustan ya zo domin yi wa duk ƴan ƙungiyar adalci.

Rahotanni sun bayyana cewa a tsakiyar watan Agustan 2026, ne dai wa'adin shugabannin ƙungiyar ta NUT, reshen jihar Kano, zai ƙare, wanda a ƙa'ida ake gudanar da zaɓe kashi uku, Kano ta Tsakiya, Kano ta Arewa da kuma Kano ta Kudu.

Sai dai shugaban ƙungiyar malamai ta ƙasa NUT, reshen jihar Kano, Kwamared Baffa Ibrahim Garko, ya ce kamata ya yi shugabannin ƙungiyar ta VCTF, su tuntuɓe ta kafin yin magana da kafafen yaɗa labarai, tunda su ne suke da alhakin sanar da su halin da ake ciki game da ƙungiyar.

Kwamared Baffa Garko, ya kuma ce da zarar lokacin zaɓen ya ƙarato za su sanar da tsare-tsare kamar yadda aka saba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM