Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta wanke Hafizin Alqur'ani, Ja'afar bisa rashin samun sa da laifin satar wayar dubu 19 a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta wanke Hafizin Alqur'ani, Ja'afar bisa rashin samun sa da laifin satar wayar dubu 19 a Kano.

Kotun majistiri da ke zamanta a Ƙaramar Hukumar Kura a jihar Kano, ta wanke Hafizin Alqur'ani, Ja'afar Abdullahi Ishaq, bisa rashin samun sa da laifin satar wayar salula ta naira dubu 19.

Kafin wanke shi, Ja'afar Abdullahi ya shafe makonni 3 yana tsare a gidan ajiya da gyaran hali a Kano.

Alkalin Kotun, Mai Shari'a Muhammad Alhaji Isa, ya wanke Ja'afar ne bayan dogon nazari da kuma bincike a kan shari'ar.

Tunda farko dai an zargi Malam Ja'afar da ƙwace wayar wani yaro da aka aika ya kai Caji a Garin Rantan na Ƙaramar Hukumar Bebeji.

Kafar GTR Hausa ta ruwaito cewa, kotun ta sallami Ja'afar Abdullahi ne bayan da ta gano cewa sharri aka yi masa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM