Za a ɗauki matakin doka kan duk wanda ya tada zaune tsaye a yankin Rimin Zakara - Kwamishina a Kano
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Ma'aikatar ƙasa da tsara birane ta jihar Kano, ta sha alwashin ɗaukar matakin doka a kan duk wanda ya nemi ta da zaune tsaye a yankin Rimin Zakara.
Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Kwamishinan ma'aikatar Abduljabbar Muhammad Garko, ne ya bayyana hakan a safiyar Alhamis 3 ga watan Satumban 2026.
Kwamishinan na wannan jawabin ne a yayin da ya goranci tawagar ma'aikatar ta ƙasa zuwa yankin Rimin Zakara, domin nuna in da iyakar garin yake da kuma jami'ar Bayero Kano.
Aƙalla dai an kwashe sama da shekaru Hamsin ana danbarwa a kan haƙƙin mallakar gurare da dama na yankin Rimin Zakara, musamman ma a tsakanin mazauna yankin da kuma Jami'ar Bayero da ke Kano.



