Koma Labarai
Labarai

Mutane sun fara barin gidajen su daga unguwar Tsamiyar Mariri, Kano, saboda zaizayar ƙasa da sauran matsaloli.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mutane sun fara barin gidajen su daga unguwar Tsamiyar Mariri, Kano, saboda zaizayar ƙasa da sauran matsaloli.

Al'ummar unguwar Tsamiyar Mariri da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, sun gudanar da zanga-zangar lumana don nuna damuwar su kan rashin al'amuran more rayuwa.

Mutanen sun gudanar da zanga-zangar lumanar ne ranar Lahadi a cikin unguwar tasu, inda suka fito kwansu da kwarkwata domin isar da sakon su ga mahukunta kan matsalolin da ke damun su.

Cikin abubuwan da suka ce na ci musu tuwo a kwarya a yankin nasu, akwai rashin magudanan ruwa da kan haifar musu da ambaliyar ruwa, da lalacewar hanyar su da ta tashi daga Tsamiyar Mariri zuwa layin mai allo, ta dangana zuwa babban titin Hotoro, al'amarin da ya haifar musu da zaizayar kasa.

Sauran matsalolin su ne rashin asibiti, da kuma rashin kayan aiki a makarantar yankin su, al'amarin da ke kawo tasgaro a harkar koyar da ƴaƴan su.

Da yake yi wa Dala FM Kano, ƙarin bayani, shugaban shirye-shirye a kungiyar samar da ci gaban unguwar Tsamiyar Mariri da ke karamar hukumar Kumbotso, Nura Isma'il Ahmad, (Yamalash) ya ce sun gudanar da zanga-zangar lumanar ne don tunawa shugabannin su matsalolin da suke damun su.

A cewar sa, "Zaizayar ƙasar da mu ke fuskanta sakamakon lalacewar hanya da rashin magungunan ruwa, yanzu haka wasu mutane sun fara tashi daga unguwar mu," in ji Yamalash.

Ya kuma ce, duk lokacin da aka yi ruwan sama mutane suna rasa hanyar da za su wuce sakamakon yadda ruwa yake cika hanya, tare da shiga gidajen mutane.

Ya kuma yi kira ga mahukunta da su kai musu ɗauki domin magance musu matsalolin da suke damun su.

Mallam Salihu, Shi ne limamin unguwar Tsamiyar Mariri, ya ce akwai abin ban mamaki kan yadda shugabannin yankin nasu suka gaza samar musu da al'amuran more rayuwa, la'akari da yadda shugabannin suka yi musu alkawari tun a lokacin yakin neman zaben 2023, amma kawo yanzu shiru suke ji.

Ready to PlayDala FM88.5 FM