Tsohon Daraktan Hukumar jin daɗin alhazai a Kano, Sani Lawal Ƙofar Mata ya rasu.

Tsohon Daraktan Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano, Alhaji Sani Lawal Ƙofar Mata, ya rasu a ranar Lahadi 20 ga watan Satumba, 2026.
Alhaji Sani Lawan Kofar Mata, ya taka muhimmiyar rawa a siyasar jihar Kano, a lokacin mulkin Malam Ibrahim Shekarau, ya rasu.
Marigayin ya kasance tsohon Darakta-Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, kuma yana daga cikin manyan ’yan siyasar da suka yi fice a jam’iyyar ANPP a Kano a wancan lokaci.
Sani Lawan Kofar Mata ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da suka yi wa gwamnatin Shekarau tasiri a harkokin siyasa, musamman a lokacin zaɓen 2007, inda rahotanni suka bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu goyon bayan Shekarau a wancan lokaci.
Za ayi jana'izarsa a gobe Litinin da karfe 9 na safe a Kano.



