Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano za ta ƙara wadata ruwa ga mazauna birnin jihar cikin mako guda

Hassan Mamuda Ya'u 46 views
Gwamnatin Kano za ta ƙara wadata ruwa ga mazauna birnin jihar cikin mako guda

Gwamnatin Jihar Kano tace, za ta ƙara faɗaɗa rarraba ruwa ga jama'a a faɗin Jihar cikin mako guda.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, ya ce ana sa ran za a ƙara faɗaɗa rarraba ruwan sha ga jama’a a faɗin jihar cikin mako guda mai zuwa.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Barka da Hantsi na gidan rediyon Freedom Radio, inda ya yi bayani kan ci gaban da ake samu wajen gyaran manyan wuraren samar da ruwa a jihar.

Ya ce gidan samar da ruwa na Challawa, wanda aka tsara zai samar da kusan kashi 51 cikin 100 na ruwan da ake buƙata a birnin Kano, na daga cikin wuraren da ake aikin farfaɗowa, tare da madatsun ruwa na Tamburawa da Goron Dutse.

Dr. Dahiru ya ce wasu tsare-tsaren samar da ruwa da suka shafe shekaru ba sa aiki yanzu suna dab da komawa aiki yadda ya kamata, sakamakon gyare-gyaren da ake yi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM