Gwamnatin Kano ta gano gine gine sama da 200 da aka yi su ba bisa ƙa'ida ba a jihar

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta dakatar da duk ginin da aka fara yin sa ba bisa ƙa'ida ba, muddin ba a nuna takardun izinin fara gini ba.
Shugaban kwamitin hana yin gine gine ba bisa ƙa'ida ba na jihar Kano, Dr. Ɗalhatu Aliyu Sani, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai a yau Juma'a 26 ga Yuni, 2026.
A cewar sa, "Daga fara aikin mu zuwa yanzu mun gano gine gine sama da 200 da aka yi su ba bisa ƙa'ida ba a Kano, musamman a yankin Kwarin Gogau da ke ƙaramar hukumar Fagge da aka yi akan kwalbati.
Ya ce sauran su ne a yankin ƙaramar hukumar Kumbotso da aka yi a kasan wayar wuta ta "High tension" sai na Ɗorayi da ake ƙoƙarin gina gidan shirya Fim ɗin Hausa.
Wakilinmu Muzammil Ibrahim Yakasai ya ruwaito cewa, Dr. Ɗalhatu Aliyu ya kuma ƙara da cewa, idan wanda yake ƙoƙarin gina gidan shirya fim ɗin Hausa a Ɗorayi wato (Film House) ya sauya manufar ginin to gwamnati za ta buɗe gidan.



