Koma Labarai
Labarai

Majalisa ta buƙaci gwamnatin Kano ta ɗauki matakin gaggawa kan cutar diphtheria, da ta kashe mutane 50 a Rano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisa ta buƙaci gwamnatin Kano ta ɗauki matakin gaggawa kan cutar diphtheria, da ta kashe mutane 50 a Rano.

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta buƙaci gwamnatin jihar nan da ta ɗauki matakin gaggawa kan ɓarkewar cutar diphtheria, wadda rahotanni suka ce ta hallaka fiye da yara 50 a karamar hukumar Rano.

Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Rano, Ibrahim Muhammad, ya ce cutar ta fi ƙamari a yankunan Rurum A da Rurum B da Sabuwar Ƙaura, inda ya buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwamishinan Lafiya na jihar, da su ƙara tura magunguna da ma’aikatan lafiya yankunan

Da suke goyon bayan ƙudurin, wasu daga cikin ƴan majalisar sun ce cutar ta bazu zuwa ƙaramar hukumar Kiru, inda ta shafi Kwarin Ɗangora da Ɗangora da Yelwa.

Wakilinmu na Sunusi Shuaib Musa ya ruwaito cewa, Majalisar ta kuma amince da ƙudirin tare da umartar kwamitinta kan lafiya da ya tattauna da ma’aikatar lafiya kan aiwatar da dokar kare lafiyar jama’a, da kuma samar da agajin gaggawa ga al’ummomin da abin ya shafa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM