Koma Labarai
Tsaro

Dattawan da aka yi garkuwa da su yayin sasanci a Zamfara sun kuɓuta bayan biyan kudin fansa milyan 35

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Dattawan da aka yi garkuwa da su yayin sasanci a Zamfara sun kuɓuta bayan biyan kudin fansa milyan 35

Rahotanni sun bayyana cewa dattawan da aka yi garkuwa da su a kauyen jihar Zamfara sun shaki iskar 'yanci, bayan an biya kudin fansar su aƙalla Naira milyan 35.

Sai dai majiyar da ta tabbatarwa kafar DCL Hausa da labarin da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce mutane uku daga cikin dattawa 50 ɗin da aka sace sun rasu a hannun masu garkuwa da su.

A ranar 8 ga Yunin, 2026 ne dai wasu dattawa daga mazabar Magamin Diddi a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, suka yi kwamiti domin zuwa neman sasanci da ɓarayin daji, amma ɓarayin suka yi garkuwa da su bayan da suka isa wurin.

Bayan shafe sama da makonni uku a hannu, dattawan sun kuɓuta bayan an biya ɓarayin dajin kuɗin fansa na kimanin Naira milyan 35.

Ready to PlayDala FM88.5 FM