Majalisa ta buƙaci gwamnatin Kano ta samar da makarantar gaba da sakandare a Ɓagwai ko Shanono.

Majalisar dokokin Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta samar da makarantar gaba da sakandare a ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin Ɓagwai ko Shanono.
Ɗan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Biyu, Ali Lawan Alhassan ne ya gabatar da ƙudirin a zauren majalisar.
Ali Lawan ya ce duba da yadda rayuwa ta yi tsada, ba kowane Uba ne zai iya biya wa yaron sa kuɗin makaranta daga Ɓagwai ko Shanono zuwa yankunan da ke maƙota ka da su ba.
Ɗan majalisar ya ce, samar da makarantar ta gaba da sakandare zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, tare da daƙile yawon cirani da mutane ke yi zuwa wasu garuruwan da sunan neman kuɗi.
Wakilinmu na majalisar Sunusi Shuaib Musa ya ruwaito cewa, ɗan majalisar ya ce samar da makarantar zai sa yankin na sa ya yi gogayya da sauran takwarorin su na shiyyoyin Kano.



