Koma Labarai
Labarai

Najeriya da Turkiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyar haƙar ma'adinai

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Najeriya da Turkiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyar haƙar ma'adinai

Ƙasashen Turkiyya da Najeriya sun sanya hannu a kan yarjejeniyar hakar ma’adinai wacce ake fatan za ta inganta haɗaka a tsakanin kasashen, wacce za ta amfani kasashen biyu.

Ministan Makamashi da Albarkatun Kasa na Turkiyya Alparslan Bayraktar da Ministan Bunkasa Albarkatun Kasa na Nijeriya Oladele Henry Alake ne suka sanya hannu a madadin kasashen nasu, yayin da Dele Alake ya kai ziyara Turkiyya don halartar Taron Ma’adinan Kasa na Istanbul Karo na biyu (INRES 2026).

Alparslan Bayraktar ya ce “mun yi imani cewa za mu bunkasa alakarmu da Nijeriya a fannin makamashi da albarkatun kasa, ta hanyar da kasashen biyu za su amfana.”

Ready to PlayDala FM88.5 FM