Bayyana Usman Ibrahim da Ƴan Sanda suka yi a matsayin wanda ake nema ya saɓa doka - Lauya a Kano
Wani lauya mai suna Barrister Shua'ibu Gama ya ayyana cewar, bayyana Usman Ibrahim a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo da yansandan shiyya ta daya (Zone One) suka yi ya saɓa da tsarin doka.
Barrister Gama ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai a ranar Laraba 23 ga watan Satumban 2026.
Lauyan ya bayyana cewar akwai umarni da babbar kotun jaha ta bayar tun a ranar 12 ga watan Agustan 2026, a kan cewar kada yansandan su kama shi, duk wani mai ƙorafi akan Usman to ya je a hadu a kotu.
Barrister Gama ya bayyana cewar dole ne sai yansanda sun girmama umarnin kotu, a bisa umarnin kotun.
A cewar sa, "Matakin da yansandan suka ɗauka a matsayin cin zarafi ga shi Usman Ibrahim, kuma ba za mu zuba ido a yi wa doka karan tsaye ba," in ji shi.
Barista Gama ya kuma bayyana cewar za su ɗauki mataki na Shari'a akan abin da yansandan suka yi.



