Koma Labarai
Tsaro

Rundunar Anti-Phone Snatching Force, ta cafke matashi da wuƙa bayan tarwatsa dilolin ƙwaya da masu faɗan daba a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rundunar Anti-Phone Snatching Force, ta cafke matashi da wuƙa bayan tarwatsa dilolin ƙwaya da masu faɗan daba a Kano

Rudunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da kuma daƙile ta'ammali da kayan maye, ta Anti-Phone Snatching Force a nan Kano, ta cafke Mustapha Isma'il, ɗauke da wata wuƙa, bisa zargin su da kitsa faɗan daba da kuma dillancin ƙwayoyi a Ƙofar Ɗan agundi.

Mai magana da yawun rundunar tsaron, Ibrahim Garba Ahmad, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, ya ce sun kama matashin ne bayan da suka samu bayanan sirri kan yadda ake sayar da ƙwayoyi da kuma harkar daba a yankin Ƙofar Ɗan agundi.

A cewar sa, "Bayan samun bayanan sirri a kan matasan ne kwamandan rundunar Nura Salisu Sharaɗa, ya tura dakarun sa ƙarkashin jagorancin DC Operation Abduljalal Sa'idu Muhammad, inda suka je tare da tarwatsa masu faɗan daba, da dilolin ƙwayar, suka kamo matashi Mustapha ɗauke da wuƙar da yake tare da ita," in ji Ibrahim.

Da yake zantawa da wakilinmu Hassan Mamuda Ya'u, matashin da aka kama ya tabbatar da samun sa da wuƙa mai kamu ɗaya da rabi, inda ya ce yana riƙe wuƙar da aka same shi da ita ne domin ya kare kansa daga maƙiya, masu kawo musu hari.

Sai ai Mustapha Isma'il ya bayyana nadamar sa bisa samun sa da wuƙar, inda ya ce da yardar Allah, wannan shi ne karo na farko ya hakuri da yawo da wuƙar.

Kakakin rundunar ta Anti-Phone Snatching Force Kano, Ibrahim Garba Ahmad, ya ce tuni Kwamandan rundunar Nura Salisu Sharaɗa ya bada umarni a miƙa matashin gurin da ya dace domin ɗaukar mataki na gaba.

Ya kuma ce rundunar za ta ƙara baza komar ta a guraren da ake hada-hadar ƙwayoyi da sayar da Tabar Wiwi, da kuma yaƙi da masu faɗan daba, da kwacen waya domin ganin an ƙara wanzar da zaman lafiya a faɗin jihar Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM