Koma Labarai
Tsaro

An cafke manyan kwamandojin Boko haram/ISWAP, 7 bayan da suka dawo daga aikin hajjin 2026.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
An cafke manyan kwamandojin Boko haram/ISWAP, 7 bayan da suka dawo daga aikin hajjin 2026.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa jami'an tsaro sun kama wasu mutane bakwai da ake zargin manyan kwamandojin ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne, bayan da suka dawo daga aikin hajji a ƙasar Saudiyya, ta filin jirgin sama na jihar Katsina.

Ministan harkokin cikin gida Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar 27 ga Yuni, 2026.

Ya yi wannan bayani ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja bayan Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya rattaba hannu kan dokar hukumar kula da bayanan shaidar katin ɗan kasa (NIMC) ta shekarar 2026.

Ministan ya ce an samu nasarar kama mutanen ne ta hanyar amfani da sabon tsarin tantance bayanan masu shiga da fita ƙasar, wanda ya haɗa da bayanan shaidar 'yan ƙasa.

Olubunmi ya kuma ce, an miƙa waɗanda ake zargin ga hukumar tsaron farin kaya ta Ƙasa (DSS) domin ci gaba da bincike.

Tunji-Ojo ya bayyana cewa wannan nasara na nuna yadda sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a fannin tantance bayanan jama'a, da tsaron iyakoki ke fara haifar da sakamako mai kyau.

Ministan ya ce sabuwar dokar za ta ƙara inganta tsaron cikin gida tare da sauƙaƙawa 'yan ƙasa samun aiyukan gwamnati a ƙasar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM