Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta ɗaure matasa 4 babu zaɓin tara kan tayar da hankalin al'umma a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta ɗaure matasa 4 babu zaɓin tara kan tayar da hankalin al'umma a Kano

Kotun majistret mai lamba 24 da ke zaman ta a Airport ɗin Mallam Aminu Kano, ta hori wasu matasa 4 da ɗaurin wata ɗaya babu zaɓin tara, da kuma ɗaurin wata 6 ko zaɓin tarar dubu 30 kowannensu.

Matasan da kotun ta hukunta sun haɗar da Aminu Nura, da Muhammad Hassan da kuma Aminu Nuhu, sai Mujahed Bello.

Haka kuma, alƙalin kotun Muttaka Abba Ɗandago, ya kuma hori matasan da ɗaurin watanno 7 ko zaɓin tarar dubu 30.

Kotun dai ta samu matasan da laifin haɗa baki da tayar da hankalin al'umma da kuma kafa ƙungiyar ƴan daba, sai kuma laifin samu da makamai.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, kotun ta kuma ayyana cewar matasan za su sanya hannu a kan cewar ba za su ƙara ɗagawa al'umma hankali ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM