Kotu ta aike da Abubakar Haladu gidan yari sakamakon zargin faɗan daba da samar da rauni a Kano

Kotun majistret mai lamba 24 wadda ta ke zaman ta a Airport ɗin Mallam Aminu Kano, karkashin jagorancin mai sharia Muttaƙa Abba Ɗandago, ta aike da wani matashi Abubakar Haladu, gidan gyaran hali bisa zargin sa da laifuka bakwai kuma ciki har da cinna wa kayan mutane wuta.
Ƙunshin zargin ya ayyana cewa laifukan da ake zargin matashin sun haɗar da haɗa baki da kafa ƙungiyar yan daba, samu da miyagun makamai, sanadin rauni, kutse, tayar da hankalin al ummah, ƙeta ta hanyar cinnawa kayan mutane wuta, da kuma laifin fashi da makami.
A yayin zaman kotun na ranar Talata 2 ga Yuni, 2026, ko da aka karanta wa matashin ƙunshin zargin zarge-zargen da ake yi masa ya musanta.
Ƙunshin tuhumar ya bayyana cewar yan sandan Kano, sun kama matashin tun a ranar 14 ga watan 3, na 2026, kuma an gano cewar shi ne jagora wajen tayar da husuma a unguwar Tudun Fulani da ke yankin ƙaramar hukumar ungogo a Kano.
Matashin mai suna Abubakar Haladu, tuni dai ya samu gurbin zama a gidan gyaran hali zuwa ranar 30 ga wannan watan na Yuni, 2026.
A yanzu haka Ƴan Sanda suna neman wasu matasa 7 ruwa a jallo waɗanda ake zargin sune abokan burminsa.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, Mai shari'a Muttaka Abba Ɗandago, ya ayyana cewar kotu ba za ta lamunci tayar da hankalin al'umma ba.

