Majalisa ta zartar da ƙudirin dokar kafa hukumar tattalin arziki ta Kano, da Gwamna Abba zai jagoranta.

Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da ƙudirin dokar kafa hukumar tattalin arziki ta jihar da Gwamna Abba Kabir Yusuf zai jagoranta.
Majalisar ta zartar da dokar kafa hukumar ne a zaman majalisar na ranar Litinin 31 ga watan Agusta, 2026, bisa jagorancin shugaban ta Hon. Jibril Isma'il Falgore.
Hukumar da ake sa ran idan Gwamnati ta amince da ita, za ta yi aiki ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da wasu daga cikin kwamishinonin sa da shugabannin ƙananan hukumomin jihar.
Kazalika, hukumar za ta tsara yadda za a samar da cigaban tattalin arzikin jihar da inganta masana'antu tare da samar da aikin yi a tsakanin matasa.
A dai zaman majalisar na ranar Litinin, ta buƙaci gwamnatin Kano da ta mayar da ilimin koyon "Computer" ya zama wajibi a makarantun Firamare da Sakandare na jihar tare da kafa ɗakunan koyar da su.
Ɗan majalisa mai wakiltar Ghari da Tsanyawa Hon. Garba Ya'u Gwarmai, ne ya gabatar da ƙudirin a gaban majalisar, inda ya ce da yawa daga ɗalibai a yanzu ba sa iya cin jarrawaba da aka yi amfani da ita ta hanyar na'ura mai ƙwaƙwalwa.
Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, majalisar ta kuma karɓi saƙon gwamnan Kano, inda ya turo da sunayen Hajiya Uwa Bello Makama, da Alhaji Auwal Ibrahim don tantancewa tare da amincewa su zama wakilai a hukumar Shari'a ta Kano.



