An yi zargin matashi ya rataye kan sa sakamakon shaye-shayen kayan maye a Kano

An yi zargin wani matashi mai suna Sagiru, mazaunin garin Ƙarfi da ke ƙaramar hukumar Kura a Kano, ya rataye kan sa lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar sa.
Wani shaidar gani da ido ya shaida wa manema labarai cewa, tunda farko ana ta neman matashin ba a gan shi ba, amma bayan kwana biyu da aka buge ƙofar ɗakin sa sai aka ganshi a rataye, ina ake zargi shi ne ya rataye kan nasa har ya mutu.
A cewar mutumin, "Matashin yana shaye-shaye don haka ne ma ba kowa ne yake iya zuwa kusa da shi ba, domin idan aka je kusa da shi ɗin yana neman illata mutum da makami, musamman ma idan ya yi shaye-shayen ya yi masa karo, in ji shi.”
Tuni dai aka yi jana'izar Marigayin kamar yadda tsarin addinin musulunci ya tanadar.
Da yake nasa jawabin, Sakataren Ƙungiyar ci gaban matasan garin Ƙarfi, Zubairu Haruna Ƙarfi, ya ce al'amarin bai zo musu da daɗi ba, tare da miƙa ta'aziyya ga iyalan Marigayin.
A cewar sa saboda illar shaye-shayen ne ma kwanakin baya aka yi taron masu ruwa da tsaki a yankin inda aka ja hankalin al'umma kan su gujewa shaye-shaye domin kaucewa fuskantar matsala.
Zubairu Ƙarfi ya kuma yi kira ga matasa da su kaucewa yin shaye-shayen kayan maye, duba da yadda take da tarin illoli, kamar yadda ta yi wa Marigayin illa, har ta yi sanadiyyar rasuwar sa.

