Ƴan bindiga sun kashe mutane 6 da jikkata 1, tare da sace Shanu da tumaki a Tsanyawa da ke Kano

Ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutane 6 a yankin Ƴan Kamaye da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano, tare da jikkata mutum ɗaya, suka kuma tafi da tarin Shanu da tumakin mutane daga yankin.
Wani mazaunin yankin mai suna Adamu Umar, ya shaidawa Dala FM Kano cewa, ƴan bindigar sun shiga yankin ne a jiya Litinin tun daga misalin ƙarfe 05:00 har zuwa 07:00 na yamma, inda suka harbi mutum bakwai.
A cewar sa, "Bayan harbin mutane bakwai ɗin nan take mutane uku suka rasu, zuwa safiyar Talatar nan kuma adadin ya ƙaru zuwa mutuwar mutane shida maza 5, mace ɗaya, yayin da ɗaya ke asibiti yana samun kulawar likitoci," in ji shi.
Ya kuma ce mazauna yankin sun matuƙar shiga tashin hankali da furgici a lokacin da lamarin ya faru, domin ƴan bindigar sun shigo a kan Babura masu ƙafa biyu guda goma wani da goyon biyu, wani baburin kuma da goyon uku.
Adamu Umar ya kuma ƙara da cewa, lokacin da lamarin ke faruwa sun yi ƙoƙarin sanar da jami'an tsaro, amma sai bayan da ƴan bindigar suka ta fi sannan suka samu damar zuwa yankin nasu.
A cewar sa, "Yanzu haka ana shirye-shiryen yin jana'izar mutane shidan da suka rasu sakamakon raunukan da suka samu a jikin su bisa harbin bindagar da aka yi musu," in ji shi.
Adamu ya ce yanzu haka mutum ɗaya yana kwance a asibiti yana karɓar agajin likitoci bisa harbin bindagar da ya samu a jikin sa.
Mazauna Ƙauyen Ƴan Kamaye da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa, sun kuma buƙaci gwamnatin Kano, da hukumomin tsaro da su kai musu ɗauki wajen ƙarfafa tsaro a yankin su, domin daƙile matsalar tsaron da ke damun su.
Sai dai har kawo yanzu jami'an tsaro da gwamnati ba su ce komai ba kan faruwar lamarin, kuma da zarar sun magantu za a ji mu da su.


