Koma Labarai
Labarai

Ku guji bada kuɗi a tsarin auren gata da gwamnatin Kano za ta yi komai kyauta ne - Hukumar Hisbah

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ku guji bada kuɗi a tsarin auren gata da gwamnatin Kano za ta yi komai kyauta ne - Hukumar Hisbah

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta gargaɗi amare da angwayan da gwamnatin jihar za ta yi wa auran gata, da su guji bayar da kudaɗe ga masu zuwa gurinsu suna karbar kudade da sunan toshin auran gata.

Mataimakin Babban kwamandan hukumar Dakta Mujahiddeen Aminuddin Abubakar ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aiko wa Dala FM, ranar Laraba 22 ga Yuli, 2026.

Ya ce komai kyauta ne a tsarin auran gatan, a don haka duk wanda ya je wajan amaran ko angwayan da sunan neman kudin toshin to su Kai shi hukumar Hisbah mafi kusa domin daukar tsattsauran matakin doka a kan koma wanene.

A cewar sa, "Tun daga batun karɓar fom, da hidimar auren da komai da komai na auren gatan da gwamnatin jihar Kano, za ta yi wa amare da angwayen komai kyauta ne," in ji Mujahideen.

Hakan dai ya biyo bayan rahotannin da hukumar ta samu cewa, an fara samun ɓata gari suna zuwa suna damfarar angwayan da amaran da sunan kudin toshin auran gatan.

Ready to PlayDala FM88.5 FM