Lokaci ya yi da za a daina sakaci da fadan daba a Kano - Human Rights

Kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Center for Human Rights and Charity development, ta ce lokaci ya yi da mutane za su kaucewa sakaci wajen bada gudunmawar su domin ganin an kawo karshen fadan daba da kwacen waya a fadin jihar.
Shugaban gudanarwar kungiyar a matakin kasa, Kwamared Tasi'u Idris Idris Soja, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, a ranar Laraba 20 ga Mayu, 2026.
Ya kuma ce samar da aikin yi ga matasa, da basu ilimi, da kuma jan su a jiki, na daga cikin hanyoyin dakile matsalar daba, da kwacen waya da kuma sha da dillancin kayan maye a sassan jihar Kano.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su kata kula da tarbiyyar ya'yansu, la'akari da yadda tabarbarewar tarbiyyar ke jefa tarin matasa cikin harkokin fadan daba, da kuma sauran miyagun laifuka.
Kwamared Tasi'u Soja, ya kuma byukaci malamai da 'yan siyasa da dukkanin hukumomin tsaro, da su kara tashi tsaye wajen yin abinda da ya dace domin ganin an kawo karshen matsalar daba, a sassan jihar Kano.



